Mayakan IS ne suka kai Hari Sana'a

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata sanarwa da ake ganin mayakan IS ne suka wallafa ta a shafin Intanet, tace bangaren kungiyar dake Sana'a ne ya kaddamar da wani harin bom na mota a babban birnin Kasar, lamarin da ya shafi mutane da dama.

Harin wanda aka kaddamar da shi kusa da wani asibitin sojoji, an ba da rahotan cewa an kai shi ne domin a sami gidajen shugabannin mayakan Houthi da dama.

Rahotannin farko sun ce mutane kusan Talatin ne suka jikkata.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba kuma, na cewa mutane da dama sun mutu.

A wani al'amarin daban kuma, wani mai magana da yawun sojojin dake kawance da mayakan Houthin, ya ce sun harba wani makami mai linzami akan wani sansanin soji dake lardin Riyadh a Saudi Arebiya.