An soma karancin man fetur a Abuja

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An soma dogayen layuka a gidajen mai

Bisa ga dukkan alamu an sake komawa gidan jiya a wasu sassan Nigeria dangane da matsalar karancin man fetur.

Mazauna Abuja, babban birnin kasar tuni suka sake koma wa cikin fama da matsalar ta karancin man fetur abin da ke jefa kunci a rayuwar al'umma.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan bumburutu na cikin karensu babu babbaka

Galibin gidajen mai sun cika da dogayen layukan ababen hawa, kuma alamu sun nuna cewa ba a sayar da man a gidajen mai da dama.

A 'yan makonnin da suka gabata an yi fama da matsalar karancin man fetur mai tsanani a duk fadin kasar.

Da zarar an soma matsalar karancin mai a Nigeria rayuwar 'yan kasar na shiga cikin mawuyacin hali kasance farashi abubuwan more rayuwa na tashin gauron zabi.