Amina Zakari ta zama shugabar INEC

Hakkin mallakar hoto inec
Image caption Hajiya AminA Zakari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada Hajiya Amina Zakari a matsayin shugabar rikon kwarya a hukumar zaben kasar.

Shugaban ya bayyana nadin ne a wata sanarwa da Haruna Imrana, daraktan watsa labarai na ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin Tarayya, ya fitar.

Imrana ya ce nadin nata ya fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Yuni har sai lokacin da aka nada shugaban hukumar mai cikakken iko.

Gabanin nadin nata, Amina Zakari, kwamishina ce a hukumar ta zaben Najeriya.

Hajiya Amina 'yar jihar Jigawa ce da ke arewacin kasar, kuma ta yi digirinta na farko ne a fannin hada magunguna na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

An nada ta kan mukamin ne bayan saukar Farfesa Attahiru Jega, wanda shi ne shugaban hukumar daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2015.