Boko Haram: Kamaru za ta sako yara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru sun sha alwashin kawar da Boko Haram

Kungiyar Amnesty International ta ce gwamnatin Kamaru na shirin sako yara kanana su 84 da ta tsare tsawon watanni shida da suka wuce.

An kama yaran ne lokacin wani samame da aka kai a wasu makarantu da ke lardin arewa mai nisa.

Hukumomin kasar sun ce ana amfani da makarantun domin horas da 'yan Boko Haram.

Kungiyar Amnesty ta ce wasu daga cikin yaran ba su wuce shekaru biyar ba.

Kazalika ta ce rabin yaran bai haura shekaru 10 ne.

Ba a gabatar da wata tuhuma ba a kan yaran bisa aikata muggan laifuka ba.