EFCC za ta gudanar da bincike a Katsina

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Hukumar binciken cin hanci a Najeriya EFCC

A Najeriya, a na tuhumar shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina dake arewacin kasar bisa zargin al'mubazaranci da kudade da yawansu ya kai naira biliyan 7 na kananan hukumomin su.

Kwamitin bincike kafin karbar mulki daga tsohowa zuwa sabuwar gwamnatin jihar ne ya gano badakalar.

Honorable Rabe Nasir, daya daga cikin 'yan kwamitin ya ce sun tura takardar koke game da batun a gaban hukumar EFCC.

Ya ce kudaden da shugabannin kananan hukumomin suka kashe sun hada da kudaden SURE-P, kuma babu wasu ayyuka na zahiri da aka gudanar da kudaden.