Sojoji sun kashe 'yan bingida 23 a Sinai

Image caption Sojojin Masar a Sinai

Sojojin Masar sun ce sun kashe 'yan bindiga 23 bayan jerin hare-hare da aka kai a kan sojoji a yankin Sinai.

An kashe ko kuma raunana sojoji 10 a wani hari a kan wasu shingayen ababen hawa 5, wanda kimanin 'yan bindiga 70 suka yi.

Rahotanni daga yankin sun ce da akwai yiwuwar adadin mutanen da aka kashe sun fi haka yawa.

Sau da yawa 'yan bindiga masu da'awar kishin musulinci suna harin cibiyoyin sojoji da na 'yan sanda a tsibirin Sinai.