Tsipras ya dage kan kuri'ar raba gardama a Girka

Alexis Tsipras, Pirayim Ministan Girka Hakkin mallakar hoto EPA

Pirayim ministan kasar Girka Alexis Tsipras ya ce, kamar yadda aka tsara, za a gudanar da zaben raba gardamar ranar Lahadi--ya kuma yi kira ga masu kada kuri'ar da su yi watsi da sharuddan da masu baiwa kasar bashi suka gabatar.

A wani jawabinsa, Mr Tsipras ya ce muddin jama'a suka zabi rashin goyon baya, hakan zai aike da sakon cewa tilas a dakatar da shirin tsuke bakin aljihu.

Sannan kuma yayi watsi da hasashen da wasu ke yi cewa hakan ka iya sa Girka ta fice daga cikin kasashe masu amfani da kudin Euro.

Ya ce '' A bayyane take ga jama'a su zabi yadda suke son rayuwarsu ta kasance a gobe, cewa a'a ba yana nufin ficewa daga Turai ba, amma dawowa Turai cikin daraja.'

Ministocin kudi daga kasashe masu amfani da kudin Euron dai sun amince da su dakatar da duk wata tattaunawa har sai kasar Girkar ta gudanar da zaben raba gardamar.