Mutane sama da 140 sun mutu a Indonesiya

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan sanda a Indonesia sunce an gano gawarwakin mutane 140 daga wani jirgin saman soji da yai hatsari a yankin Sumatra a ranar Talata

Babu dai wanda ya rayu a cikin jirgin, sannan wasu mutanen 20 sun mutu a kasa, a lokacin da jirgin ya fada a kan wani bangare na birnin Midan.

Ba a san ko menene ya janyo hatsarin jirgin ba, wanda ya faru jim kadan bayan tashin sa.

Yawancin mutanen da ke cikin jirgin dai 'yanuwan sojoji ne da aka sake musu wuraren aiki.

Wannan shi ne hatsarin jirgi na hudu da ya shafi sojojin Indonesiya cikin shekaru uku, kuma mutanen kasar da dama na neman ganin an inganta kayayyakin ake amfani da su a cikin kasar wajen harkar tsaro.