An gano gawarwaki 141 a jirgin daya fado

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin sojin kasar Indonesia da ya yi hadari

'Yan sanda a Indonesia sun ce an gano gawarwakin mutane 141 daga jirgin sama na soji da ya yi hadari ranar Talata a Sumatra.

Babu ko mutun daya da ya tsira da ransa a cikin jirgin, sannan akwai wasu mutanen gari kimanin 20 da suka mutu bayan jirgin ya rikito a inda suke a birnin Medan.

Kawo yanzu dai, babu cikakkiyar masaniya game da abinda ya haddasa hadarin wanda ya auku jim kadan bayan jirgin ya tashi.

Wani babban jami'in sojin saman Indonesia, Air Marshall Supriantna ya ce matukin jirgin ya nemi izini akan ya juya da jirgin zuwa inda ya taso saboda wasu matsaloli a jikin jirgin.

Wani mai magana da yawun sojin sama na kasar Dwi Badaramoto ya ce akwai jamian soji a cikin jirgin, da kuma iyalan su.

Jirgin da yayi hadirin a jiya, tun a shekarar ta 1964 yake zirga zirga.