Zaftarewar kasa ya hallaka mutane a Indiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zaftarewar kasa a Indiya

Zaftarewar kasa da ta auku sakamakon ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 21 a yankin Darjeeling da ake noman ganyen shayi a Indiya.

Wani jami'in yankin ya gayawa kamfanin dillanci ta AFP cewa a garin Mirik da Kalinpong in da zaftarewar kasar ya fi kamari, tohowar ruwa da laka da karfi ya "ture abubuwa daga in da suke".

A halin yanzu, mutane da dama sun bata kuma ana tsoro yiwuwar makallewar wasu a laka da braguzan gini da wasu tarkacen.

Babban titin da ke hada yankuna masu tsaunuka da kuma cikin gari ya katse gaba daya kuma daruruwan masu yawon bude ido suna cikin wadanda suka makale.

An yi kira ga sojoji domin su kai dauki.