Buhari ya gargadi hukumar aikin hajji

Image caption Shugaba Buhari ba ya shiri da masu rashin gaskiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi hukumar alhazzai ta kasar da ta tabbatar ta kawar da duk wani aikin rashin gaskiya da cin hanci da rashawa da ake yi a cikin harakar ta aikin hajji gabanin somawar aikin hajjin a watan gobe.

Shugaba Buhari ya yi wannan gargadin sa'adda ya gana da shugaban hukumar, Alhaji Abdullahi Mukhtar Mohammed a fadarsa da ke birnin Abuja.

"Shugaban kasa ya amince da abubuwan da muka gabatar masa domin samun nasarar aikin hajjin bana," in ji Mohammed.

A cewarsa, shugaba Buhari ya jaddada cewa duk abin da ya shafi rashin gaskiya hukumar aikin hajjin ta tabbatar da ta dauki mataki a kai.

Ana saran mutane 76,000 za su gudanar da aikin hajji a bana daga Nigeria.