Yarima Alwaleed zai sadaukar da $32 biliyan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yarima Alwaleed bin Talal

Wani hamshakin attajiri dan kasar Saudiyya, Yarima Alwaleed bin Talal ya sha alwashin sadaukar da dukiyarsa da ta kai dala biliyan 32 a cikin shekaru masu zuwa.

Yarima Alwaleed babban dan kasuwa ne wanda ke rayuwar kasaita.

Ya samu arzikinsa ne ta hanyar gina gidaje, da kafafen yada labarai, da kuma sa hannun jari a kamfanoni kamarsu Twitter da Apple.

Yarima Alwaleed kuma yana da otal-otal a biranen New York, da Paris.

A cewarsa, Bill Gates ne ya tsima shi, abin da kuma ya sa shi alwashin sadaukar da dukiyarsa.

Yariman ya ce zai yi amfani da dukiyar tasa wajen ayyukan kawar da cututtuka, da kuma agaji daga bala'o'i, da kuma 'yancin mata.