Wasu bankuna sun bude a Girka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu bankunan su bude a Girka

An bude wasu bankuna a Girka saboda masu karbar fansho wadanda basu da katin cire kudi.

An fara kafa layi tun da sassafe kuma ana takaitata adadin mutanen da ake bari su shiga bankuna amma wakilin BBC da ke garin Athens ya bayyana cewar mutane na bin layi cikin tsanaki.

An rufe bankunan a lokacin da babban banki Tarayyar Turai ya dakatar da basu kudaden gaggawa da ya taimakawa kasar a baya.

Bankin ya yanke shawarar yin hakan ne bayan da Athens ta kammala magana da masu basu bashi kuma suka sanar da neman ceto a kan kuri'ar raba gardama na baya-baya nan.

A ranar laraba ne ake sa ran Babban bankin tarayyar turai zai tattauna kan batun kudaden nan gaba a yau.