PDP ta nemi a cire Amina Zakari

Hakkin mallakar hoto inec
Image caption Amina Zakari ce ta gaji Jega

Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani ga zargin da jam'iyyar adawa ta PDP ta yi cewa shugaba Muhammadu Buhari bai bi ka'ida ba wajen nada Amina Zakari a matsayin mukaddashin shugabar hukumar Zaben kasar.

A ranar Laraba ne dai jam'iyyar PDP ta zargi shugaba Buhari da nada Amina Zakari a kan mukamin domin cimma wata boyayyar manufa ta sa, a don haka kuma ta bukaci da a sauke ta daga kan mukamin.

Sai dai a martanin data mayar, Fadar Shugaban kasar ta ce zargin na jam'iyyar PDP ba shi da tushe balle makama.

Nadin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa Amina Zakari a matsayin mukaddashin shugabar hukumar zaben kasar, bayan wa'adin shugabancin Farfesa Attahiru Jega ya cika, ya bar baya da kura, musanman ma ga jam'iyyar adawa ta PDP.