Ana fatattakar mayakan IS a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin kasar Masar

Jami'an tsaro a Masar suna ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar IS da suka far ma yankin arewacin Sinai na kasar.

Rundunar sojin kasar ta ce ba zata daina bude wuta a kan wadanda ta kira 'yan ta'adda ba har sai ta kawar da su daga yankin.

Jiragen sama na yaki a Masar sun ci gaba da lugudan wuta a daren Laraba, kwana daya bayan wani kazamin fada daya barke ya yi sanadiyar mutuwar mayakan da dama.

Wannan dai shi ne harin da suka kai da yafi daukan lokaci kuma a wurare da yawa, da suka hada da wuraren duba ababen hawa, da ofishin 'yan sanda da kuma garin Sheikh Zuwaid.

Kakakin sojin kasar Brigadiya Mohammed Samir ya ce sun kashe akalla mayakan kungiyar 100.