Sojojin Masar sun kwato ikon Sinai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Masar

Sojojin Masar sun ce sun kwato ikon arewa masogabashin tsibirin Sinai bayan wani babban hari da ga mayakan masu ikirarin kishin Islama suka kai wa tsibirin.

'Yan bindigar sun kai harin kunar bakin wake a kan sansanonin soji a wani kazamin fada da aka shafe ranar laraba na yi.

Rundunar soji sun ce an kashe sojoji 17 kuma ankashe 'yan bindiga fiye da 100.

Wasu majiyoyi sun yi hasashen cewa adadin jami'am tsaro da suka mutu ya fi haka.

Wani wakilin BBC da ke Alkahira ya ce farmaki na kungiyar IS ya sa an fara nuna tantama a kan ko sojojin za su iya kawo karshen ta'adanci.