Kwankwaso ya kai EFCC gaban kuliya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kwankwaso ya kasa fita daga gidansa a Abuja

Wata babbar kotu a jihar Kano ta ki amincewa da bukatar da tsohon gwamnan jihar Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya shigar gaban ta yana neman ta hana hukumar yaki cin hanci da rashawa EFCC kama shi.

Kotun da ke zama a garin Gezawa ta bukaci kada a dauki wani mataki kan gwamnan har sai kotun ta saurari bangarorin da ke da ruwa da tsaki a ranar 15 ga watan gobe.

Wasu 'yan Fansho ne a jihar Kano suka shigar da karar tsohon Gwamna Kwankwaso gaban hukumar EFCC suna zargin sa da yin almabazaranci da kudin 'yan fanshon a zamanin da yake gwamna.

A zaman kotun da aka yi da farko a cikin makon nan, lauyan tsohon gwamnan ya shedawa kotun cewa, wanda yake karewa ba ya iya fita daga gidan sa a Abuja saboda tsoron ka da EFCC ta kama shi, abin da lauyan ya ce hakan tamkar tauyewa tsohon gwamnan yancin sa ne.