An hallaka mutane kusan 50 a Monguno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kona kauyuka da dama a Borno

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria na cewa mayakan Boko Haram sun kai hari inda suka hallaka mutane 48 a kauyuka biyu a karamar hukumar Monguno.

Dan majalisa da ke wakiltar yankin, Mohammed Tahir Monguno ya shaida wa BBC cewa tun a ranar Talata mayakan Boko Haram din suka kaddamar da harin a lokacin mutane suna Sallah.

Wani mazaunin garin Monguno a hirarsa da BBC ya ce "Mutanen da aka kashe sun fi 50.Mutane na Sallah suka jira su sannan su raba maza da mata kafin su ('yan Boko Haram) hallaka mazan."

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji sun ce suna iyaka kokarinsu domin kawar da Boko Haram

"An dauko wadanda suka ji raunuka a cikin baro zuwa garin Monguno, na ga mutane biyar wadanda aka harba da bindiga," in ji mutumin.

Bayanai sun nuna cewa dakarun gwamnati sun ci karfin 'yan Boko Haram a 'yan watannin da suka wuce amma hakan bai hana 'yan kungiyar kaddamar da hare-hare ba.

Shugaba Buhari ya dauki alkawarin muskushe 'yan Boko Haram a bikin rantsar da shi a karshen watan Mayu.