'Yan majalisa sun kai wa Buhari kukan su

Image caption Har yanzu abubuwa ba su daidaita ba a majalisun dokokin Nigeria

Wata tawagar 'yan majalisar wakilan Najeriya ta yi ganawar sirri da shugaban kasar Muhammadu Buhari a fadarsa, domin neman ya sa bakinsa a irin rikicin shugabancin da ya dabaibaye majalisun dokokin kasar.

Ganawar da aka yi a daren ranar Laraba, na zuwa ne a daidai lokacin da majalisun dokokin kasar biyu ke cikin wani halin rudani sakamakon ja-in-jar da ta biyo bayan zaben shugabannin majalisun.

Daya daga cikin 'yan majalisar, Honourable Magaji Da'u Aliyu ya shaida wa BBC cewa "ya kamata shugaban kasa ya ji kowanne gefe (a wannan rikici); ya ji wadancan('yan bangaren kakakin majalisar), yanzu ya saurare mu. Mu 173 ne muke tare da shi (Buhari); su kuma 30 sun bar gidansu, shi ne muka gaya masa lallai ya gaya musu su dawo gida".

A bangare guda kuma shi ma shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Bukola Saraki ya kira wani taron manema labarai, inda ya nisanta kansa da zargin da ake yi masa na hada baki da jami'iyyar adawa ta PDP.

A cewar sa, shi da magoya bayansa sun zabi jam'iyyar APC a lokutan zabe, kuma ba shi da niyyar sauya sheka daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar PDP.