Lawal Daura ya zama sabon shugaban SSS

Image caption SSS ne ke da alhakin lura tsaron cikin gida a Nigeria

Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya nada Lawal Musa Daura a matsayin sabon Darekta Janar na hukumar tsaro ta farin kaya watau SSS.

Babban jami'i a ofishin shugaban ma'aikantan kasar, Imarana Haruna a cikin wata sanawar, ya ce Lawal Daura ne ya maye gurbin Ita Ekpenyong.

Lawal Musa Daura ya soma aiki ne hukumar ta SSS a shekarar 1982 kafin ya zama Darekta a wurin.

Ya yi aiki a fadar shugaban kasa sannan ya shugabanci hukumar SSS a jihohin Kano, Sokoto, Edo, Lagos, Osun da kuma Imo.

A shekara ta 2010 ne tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya nada Mr. Ekpenyong a matsayin shugaban SSS.