Kokarin cimma matsaya kan nukiliyar Iran

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wurin da Iran ke adana makamin nukliya ta

Kasashe masu karfin fada- a - ji na duniya sun kara kaimi a wajen amfani da diflomasiya a birnin Vienna a kokarin cimma matsaya kan makamin nukliya da kasar Iran gabanin sabon wa'adin da zai zo karshe a makon gobe.

Jami'in hulda da kasashen waje na kungiyar tarayyar turai tare da ministocin harkokin waje na Faransa da China za su je wajen tattaunawar da za a yi ranar Alhamis a kasar ta Austria.

Kazalika shugaban hukumar da ke kula da makamin nukiliya na majalisar dinkin duniya ya na kasar Iran domin ya samu damar aikawa da masu sa ido zuwa wuraren da makaman nukliya na Iran suke, wanda wani batu ne da ake ganin yana da muhimmanci domin a cimma matsaya.