Ana mummunan arbatu a birnin Aleppo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun gwamnati na cikin tsaka me wuya

Jiragen yakin kasar Syria sun jefa bama-bamai a kan 'yan tawaye domin dakile yunkuri mafi kamari kawo yanzu na kame birnin da ya fi girma a kasar na Aleppo.

Bangarorin biyu sun yi musayar wuta da manyan bindigogin atilare.

Wani kawancen kungiyoyin masu kishin Islama 13 da suka hada da kungiyar Syria mai alaka da Al-Qa'ida sun kaddamar da wani shiryayyen farmaki tare da aniyar kwace birnin, tare da ayyana shari'ar musulunci.

Hukumomin Syria sun ce mayakan 'yan tawaye akalla 100 ne aka kashe kafin a kora su baya.