APC za ta gana kan 'yan majalisa

Image caption Jam'iyyar ta fada rikici ne tun bayan zaben da aka yi na shugabannin majalisar dokokin kasar.

A ranar Juma'a ne ake sa ran kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya zai gana da 'ya'yan jam'iyyar domin warware takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa dangane da rikicin jagoranci a majalisun dokokin kasar.

A kwanakin baya ne rikici ya barke a majalisar wakilan kasar a kan nadin shugabannin majalisar.

Al'amarin dai ya samo asali ne bayan da shugaban majalisar, Yakubu Dogara ya ki yarda ya karanta wasikar da jam'iyyar ta APC ta aike masa wadda take kunshe da sunayen mutane hudu da take son a bai wa mukamai a majalisar.

Sai dai kakakin Majalisar Wakilan, Yakubu Dogara ya ce ya ki karanta wasikar ne saboda wata kara da wasu 'yan majalisar suka shigar gaban kotu da ke neman a dakatar da shi daga karanta wasikar.

Yayin da jam'iyyar take kokarin ganawa da 'ya'yan nata, wasu matasa na jamiyyar ta APC kuwa sun yi barazanar yin zaman dirshan a ofishin jam'iyyar idan har shugabanin jamiyyar suka kasa shawo kan matsalar da ta dabaibaye majalisar.

Al'amarin dai ya samo asali ne bayan da shugaban majalisar, Yakubu Dogara ya ki yarda ya karanta wasikar da uwar jam'iyyar APC mai mulki ta aike masa wadda take kunshe da sunayen mutane hudu da take son a ba wa mukamai a majalisar.

An dade ana ta kiraye-kiraye ga shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da ya tsoma baki dangane da rikicin.