Mutane 10 sun mutu a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption 'Yan Boko Haram

Hare-haren kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya ya kashe a kalla mutane 10 a ranar alhamis da rana, 'yan sanda jihar Borno inda lamarin ya faru sun ce harin baya-bayan nan na daga cikin hare-haren da ake zaton kungiyar Boko Haram na kaiwa kullun.

Wani jami'in 'yan sandan Jihar Aderemi Opadokun ya ce: "Wata 'yar kunar bakin wake ta yi sanadiyar mutuwar mutane 7 kuma mutane 13 sun jikkata a wani hari da ta kai kauyen Malari da ke kan babbar hanyar Bama zuwa Konduga yayin da wata 'yar kunar bakin wake ta biyu ta kashe mutane 3 a wani harin a kan hanyar".

Wata majiya ta soja ta ce a hare-haren da aka kai 'yan kunar bakin waken sun hari inda mutane suka fi yawa inda ake sayar da kayan lambu a kan babbar hanyar kudu maso gabashin Maiduguri.

Duban mutane sun mutu yayin da wasu miliyan 1.5 suka bar gidanjen su sakamakon hare-haren Boko Haram da aka shafe shekaru 6 suna yi domin kafa daular muslinci a arewa maso gabashin Afrika mai arzikin man fetur.

Kungiyar Boko Haram ta karbe wani yanki wanda girma shi ya kusa girman kasar Belgium a karshen shekarar 2014 kafin wani farmaki da sojoji suka yi suka kwace mafi yawan yankunan a farkon wannan shekarar.