Buhari ya gargadi 'yan jam'iyyar APC

Image caption Buhari ya bukaci 'yan APC su mayar da wukar

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin jam'iyyar APC su gaggauta sasanta sabanin da ke tsakaninsu don 'yan kasar su huta da takaici.

Shugaban kasar ya yi magana ne a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar, wanda aka yi a Abuja, babban birnin kasar, inda ya yi gargadin cewa jam'iyyar APC ta ci yakin neman zaben kasar, amma rikicin cikin gida na neman cinye jam'iyyar.

Ya ce alkawarin sauyin da suka yi wa 'yan Najeriya shi ne gaba da duk wani burin 'ya'yan jam'iyyar, don haka ya zama wajibi su shawo kan rikicin da ke jam'iyyar ke fama da shi domin su samu sukunin sauke wannan nauyin.

Duk da cewa Shugaban kasar bai kira suna ba a cikin jawabin nasa, amma babban rikicin da ke gaban jam'iyyar shi ne sabanin da aka samu tsakanin jam'iyyar da wasu 'ya'yanta wajen zabar shugabannin majalisun dokokin kasar.

Kuma wannan dai shi ne karon farko da shugaba Muhammadu Buhari ya yi tozali da shugabannin Majalisar Dokokin Najeriya da ake takaddama a kansu, wato Senata Bukola Saraki da Yakubu Dogara.

Yayin da jam'iyyar APC ke fatan sasanta rikicin da ya dabaibaye ta cikin gaggawa, Senata Bola Ahmed Tinubu wanda jigo ne a cikin jam'iyyar, wanda kuma wasu ke ganin yana da tasiri a kan dambarwar da ake fama da ita a majalisar dokokin bai halarci taron ba, alamar da masana ke cewa har yanzu tsuguno bai kare ba.

Image caption Kujerar Yakubu Dogara na daga cikin abin da ake takaddama a APC