Farfadowa daga ambaliyyar ruwa a Accra

Al'ummomin babban birnin Ghana, Accra, suna kan farfadowa daga matsanancin amabaliyar ruwa da na gobara da suka shafi cikin garin wata daga da ya wuce.

Mutane 150 ne suka mutu a lokacin da aka yi ambaliyar ruwa da kuma fashewa a wani gidan mai da ke unguwar Adabraka.

Hakkin mallakar hoto Anny
Image caption Roslyn Tay mai shekaru, 44, tana sayar da abubuwan abinci da ake yi da fulawa a kusa da gidan man. Ta tuna an fara ruwan sama da karfe 17:30 a ranar uku ga watan Yuni kuma an shafe sa'o'i masu yawa a na yi wanda ya jawo ambaliyar ruwa a filin gidan ta. Ita da ma'aikatan ta sun fake a jikin wani bango domin kariya. Sai kuma ta lura da man fetur a kwance a saman ruwan.
Hakkin mallakar hoto Anny
Image caption Ba a gyara ginin gidan man ba balle kwashe motocin haya da su ka kama da wuta.
Hakkin mallakar hoto Anny
Image caption Direban motar haya, Aggudey yana daga cikin wadanda suke fake a gidan sayar da man fetur bayan da suka makalle. Da gobarar ta tashi, sai ya shige cikin ruwan domin ya kare kansa amma kuma da fito sama domin ya sha iska, sai fuskar sa ta kama da wuta wanda ya jawo mishi tsananin kuna.
Hakkin mallakar hoto Anny
Image caption Rukunin gidaje inda mutane 50 ke zaune sun lalace a gobarar kuma har yanzu ba'a gyara su ba.
Hakkin mallakar hoto Anny
Image caption Tun lokacin da a ka yi ambaliyar, jami'an gwamnati sun rika rusa gidajen da aka gina kusa da hanyoyin ruwa ba bisa ka'ida ba, suna masu cewa suna cikin dalilan da suka sa ake yin ambaliyar ruwa.