An damke wasu 'yan Hamas a Falasdinu

Image caption Dakarun Falasdinawa sun hada kai da Isra'ila saboda 'yan Hamas

Dakarun tsaron hukumar Falasdinawa sun kama 'yan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a yankin gabar yamma ta Kogin Jordan.

Wannan ne kame mafi girma a cikin shekaru da yawa.

Hukumar Falasdinawa wadda jam'iyyar Fatah mai adawa da Hamas ta yi wa kaka gida, ta ce manufar ita ce ta hana Hamas yin zagon kasa ga tsaron yankin.

Wani kakakin Hamas ya bayyana kamen a matsayin wani kokari na hana wani jerin miyagun hare-hare a kwanan nan kan 'yan Isra'ila da ke a yankin yamma na gabar kogin Jordan, sannan kuma ya zargi hukumar Falasdinawa da yin aiki a madadin Isra'ila.

Wakiliyar BBC ta ce batun hadin kan tsaro tsakanin Isra'ila da dakarun hukumar Falasdinawa dai abu ne da yake da babbar sarkakiya.

Bayan samamen, an bayar da sammacen kama manyan 'yan kungiyar Fatah a yankin zirin Gaza da Hamas ke jagoranta.