Nigeria ta sanar da kudin kujerun Hajji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Miliyoyin Musulmai ne daga fadin duniya ke yin aikin Hajji a duk shekara.

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta fitar da kudin kujerun aikin Hajji na shekarar 2015.

A watan sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Uba Mana, ya aikewa kafafen watsa labarai a Abuja ranar Alhamis, ya ce masu tafiya Hajji daga arewacin kasar za su biya N758,476.59 a matsayin kudin karamar kujera da guziri $750; haka kuma matsakaiciyar kujera kudin ta shi ne N798,476 da kudin guziri $1,000; yayin da babbar kujera kudin ta shi ne N897,476 da guzirin $1,500.

A cewar sa, masu tafiya Hajji daga kudancin kasar za su biya kudin karamar kujera N766,556 da kudin guziri $750-dollar; matsakaiciyar kujera kuwa za a biya N806,556, sannan kudin guzirin ta shi ne $1000; sai babbar kujera wacce za a biya N905,556 da guziri $1,500.

Alhaji Uba Mana ya kara da cewa akwai bukatar maniyyata su biya kudadensu da wuri domin a samu damar gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin ba tare da matsala ba.

Najeriya dai na cikin kasashen da kusan kowacce shekara sai sun fuskanci kalubale game da tafiya aikin Hajji.