'Yan mata sun kai harin kunar bakin wake

Hakkin mallakar hoto

Wasu mata shidda 'yan kunar bakin wake sun kashe mutane da dama a kauyen Zabarmari da ke kusa da Maiduguri, a jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriyar ta ce cikin wadanda aka kashen har da soja daya.

Mazauna garin sun ce an kai harin ne ranar Juma'a da yamma.

Wata daga cikin 'yan kunar bakin waken ta yi kokarin shiga masallaci a lokacin da ake sallar tarawihi, inji su.

Sun ce 'yan Boko Haram sun kai ma garin hari ne da bindigogi, suna harbin mutane, suna kuma fasa shaguna suna kwasar abinci.

Sun ce sa'adda mutane ke kokarin tserewa ne sai 'yan mata 'yan kunar bakin wake suka je tasha daure da bama-bamai a jikinsu suna tayar dasu, inda suka kashe kansu da kuma mutane da dama.

Da farko 'yan Boko Haram sun fatattaki jami'an tsaron da ke kauyen, amma daga baya an tura karin jami'an tsaro wadanda su ka yi nasarar korar su, inji shedu.

Jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (wato NEMA) mai kula da shiyyar arewa maso gabashin kasar, Mohammed Kanar, ya gaya wa BBC cewa mazauna kauyen da dama sun tsere zuwa cikin birnin Maiduguri.

Ya kuma ce hukumar na kokarin ta tallafa masu.

Ya ce za a samar wa wasunsu matsugunni a sansanonin 'yan gudun hijira da ke Maiduguri, wadanda kuma ke son komawa gida, za a maida su.

Yawan hare-haren 'yan Boko Haram dai ya karu sosai cikin 'yan kwanakin nan a Najeriya.

An kuma kiyasta cewa cikin kwanaki ukkun da suka wuce kadai 'yan Boko Haram sun kashe kimanin mutane 200 a jihar Borno.

Karin bayani