Kano: Manoma sun koka kan rabon taki

Image caption Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Manoman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun koka dangane da aniyar gwamnatin na rabon taki ta hanyar kai wa mazabu.

A baya dai ana raba takin ne ta hanyar tsarin wayar tafi-da-gidanka.

Korafin da manoman suke yi dai shi ne idan aka ce za a kai takin zamanin zuwa mazabu to 'yan jam'iyya mai mulki ne kawai za su samu.

Sai dai kuma gwamnatin ta musanta hakan a inda ta ce za a kai takin zamanin mazabu ne a domin mutane su yi saurin samu kafin damina ta kankama.