Girka:Jama'a sun yi watsi da tallafin ceto

Hakkin mallakar hoto Getty

Yayinda aka kidaya kashi biyu cikin kashi uku na kuri'un da aka kada na zaben raba gardama, sakamakon ya nuna jama'a sun yi watsi da tallafin ceton.

Alkaluman da ma'aikatar cikin gida ta wallafa sun nuna masu adawa sun sami kashi 61cikin dari, wadanda ke goyon baya kuma kashi 39 cikin dari.

Gwamnatin Girkar ta jam'iyyar Syriza ta ce kin amincewar zai karfafa matsayinta wajen shawarta yarjejeniya mai armashi tana mai cewa ka'idojin tallafin zai tozarta jama'ar Girka.

Masu goyon baya kuma na gargadin cewa hakan na iya kaiwa ga ficewar Girkar daga cikin rukunin kasashe masu amfani da kudin bai daya na euro.