An caccaki Al-sisi kan sabuwar doka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan jarida na kallo dokar a matsayin tauye musu hakkinsu

Kungiyar 'yan jarida a Masar ta yi gargadin cewar wata sabuwar dokar yaki da ta'addanci, za ta kara zaizaye 'yancin fadar albarkacin baki.

Dokar za ta haramtawa 'yan jarida bayar da rahoton bayanan da suka saba wa sanarwar gwamnati a kan artabu tare da 'yan gwagwarmaya.

Duk wanda ya bayar da rahoton alkaluman wadanda suka tabu sakamakon ire-iren wadannan hare-hare da ba su yi daidai da alkaluman gwamnati ba, zai iya fuskantar daurin shekaru biyu a gidan yari.

Haka kuma daftarin dokar zai gaggauta yi wa wadanda ake zargi da ta'addanci shari'a.