China: Dabbobi za su tsinkayi girgizar kasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption China suna amfani da dabbobi domin hango lokacin da girgizar kasa za ta auku.

Rahotanni sun ce masana Kimiya a kasar China suna amfani da dabbobi domin hango lokacin da girgizar kasa za ta auku.

A shafin intanet kuma, wasu rahotannin sun bayyana cewa masana ilimin girgizar kasa a Nanjing babban birni a gabashin yankin Jiangsu, sun kafa cibiyoyi guda bakwai a gidajen ajiye namun daji dake yankin.

Cibiyoyin za su rika lura da canji a halayyar dubban dabbobi, wanda zai iya nuna alamun afkuwar girgizar kasa.

Wani wajen shakatawa, wanda ke gundumar Yuhuatai ya zama daya daga cikin cibiyoyin da ake lura da afkuwar girgizar kasa da kaji 2,000 da Aladu 200 da kuma kifaye da aka yi wa wurin ajiya.

An kafa na'urar daukar hoto a zagayen wurin shakatawar, kuma ma'aikatan za su rika kai rahoton halayyan dabbobin.

'Halayyan Dabbobin'

"Wani lokaci Dabbobi na nuna rashin sukuni kafin girgizar kasa ta faru," in ji Zhao Bing, shugaban ofishin saka idanu a yanayin afkuwar girgizar kasa.

Bing ya kara bayanin cewa, "Amma ba wai kawai domin an ga wata kaza tana nuna wasu canji a halayya kadai ke tabbatar da matsala ba, ana ganowa ne idan an kara kallon halayyar taron dabbobi ne dayawa."

An dade ana zargin cewa sauyi a halayyar dabbobi na iya nuna alamun afkuwar girgizar kasa.

A shekara 2011, masana kimiyya sun ce dabbobi na iya gano sauyi a sinadaran ruwan cikin kasa, wanda ke nuna alamun girgizar kasa.

An dauko binciken ne daga tarin kwadi da suka kauracewa kandami kwanaki dayawa kafin girgizar kasa kimanin grirma 6.3 ya afkawa birnin L'Aquilla da ke kasar Italiya.

Wani binciken ma ya nuna sauyi a halayyan namun daji makonni uku kafin girgizar kasa a kasar Peru, mai kimanin karfin 7.0 a shekarar 2011.