Dandalin zumunta na jawo sakin aure a China

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dndalin sada zumunta na jawowa ma'aurata matsaloli a China

Rahotanni a China sun ce mai yiwuwa yawan amfani da dandalin sada zumunta yana taimakawa wajen yawan sake-saken aure da ake yi a kasar.

Rahotannin sun ambato lauyoyi wadanda suka zargi ma'aurata da shafe lokuta da dama suna hira a dandalin sada zumunta na zamani a maimakon yin hira da junansu.

Sababbin alkaluma da gwamnati ta fitar a bara sun nuna cewar sake-saken aure na karuwa bayan an samu yawan sake-saken da aka samu shekaru goma da suka wuce.

Wasu dalilan kuma sun hada da tsarin saki mafi sauki da kuma abin da ake kira "sakin bogi" inda ma'aurata suke rabuwa domin su kaucewa wasu dokoki na aiki, misali na kadarori ko samun shiga makaranta sai kuma su sake daura aure.