Ministan kudin Girka ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ministan kudin Girka

Ministan kudin Girka Yanis Varoufakis ya yi murabus daga mukaminsa.

Ministan ya ce wasu 'yan kungiyar tarayyar turai ne suka nemi ya ajiye aikin nasa kuma firai ministan kasar ta Girka, Alexis Tsipras ma ya ce hakan zai taimaka wa kasar wajen cimma matsaya tsakaninta da kasashen tarayyar ta turai.

Shugabannin kasashen tarayyar turai na tunanin yin fatali da sakamakon zaben kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar a Girka a inda 'yan kasar suka zabi kin amincewa da sharuddan tarayyar na ceto tattalin arzikin kasar.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta gana da takwaranta na Faransa Francois Hollande ranar Litinin, sannan kuma akwai taron kungiyar kasashen da ke amfani da kudin bai-daya na yuro wanda za a yi ranar Talata.

Fiye da kashi 60 cikin 100 na sakamakon kuri'un da aka kada ne ya nuna cewa 'yan kasar ta Girka sun zabi kin amincewa da sharuddan tarayyar turai.