El-Rufai ya soke asusun hadin gwiwa

Image caption Gwamna Nasir El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya soke asusun hadin gwiwa tsakanin gwamnati jiha da ta kananan hukumomi.

El-Rufai a lokacin bikin rantsar da kantomomin kananan hukumomin jihar, ya ce daga yanzu za a dinga bai wa kananan hukumomin kudadensu kai tsaye ba tare da gwamnatin jiha ta taba ba.

Abin da hakan ke nufi shi ne kananan hukumomi a jihar Kaduna za su zama masu cin gashin kansu, ba tare da gwamnatin jiha ta taba kudaden da suke samu daga asusun gwamnatin tarayya ba.

Batun asusun hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi ya dade yana jan hankali, saboda ana zargin gwamnoni da wawuro kudaden kananan hukumomi, zargin da suka musanta.

Gwamna El-Rufai ya kasance na farko tun bayan da aka rantsar da sabuwar gwamnati a cikin watan Mayu, da ya sanar da bai wa kananan hukumomi damar cin gashin kansu.