An kai harin kunar bakin wake a Kano

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan sanda a Kano a Nigeria sun tabbatar da cewa wata yarinya da ta kai harin kunar bakin wake a daidai shataletalen 'Dangi' ta rasa ranta, sai kuma mutum guda da ya jikkata.

Harin ya auku ne wasu 'yan mintina bayan kammala sallar Taraweeh a wani masallaci da ke kusa da shataletalen ranar Litinin.

Wakilin BBC Yusuf Yakasai a Kano ya ce ya ga motocin daukar marasa lafiya da kuma 'yan sanda a inda aka kai harin.

Wani ganau ya shaidawa wakilinnamu cewa yaga wata yarinya a lokacin da take barin masallacin bayan kammala sallae, sannan bayan fashewar bam din, ya ga sassan jikinta a kasa.

Ya ce wani mutum ya jikkata a lokacin da yake kokarin tserewa.