An sanyawa Gimbiya Charlotte albarka

Image caption Duk da cewa makonnin ta 9 a duniya, gimbiya Charlotte ita ce ta hudu a jerin masu jiran gadon sauratar Biritaniya

Duk da cewa makonnin ta 9 a duniya, gimbiya Charlotte ita ce ta hudu a jerin masu jiran gadon masarautar Biritaniya.

Sauraniya da wasu 'yan gidan sarautar sun halarci bukin sakawa gimbiya Charlotte suna a Norfolk.

Duban mutane ne suka hallara domin su gai da 'yan gidan sarauta a wajen cocin St Mary Magdalene. Yerima Wlliams da matarsa sun zaba wa gimbiyar iyayen daki har biyar.

Image caption Yarima William ya daga wa taron hannu a yayinda ya ke rike da Yarima George.
Image caption Mahaifiyar Charlotte ce ta shiga da ita cikin cocin.
Image caption Yarima George ya yi magana da mahafiyar karkarsa - wato sarauniya
Image caption Sarauniyar da minjinta sun gaisa da taba-kunnensu.
Image caption Yerima George ya rike hannun babansa kam.