Sudan: An yi wa 'yan adawa bulala

Hakkin mallakar hoto AFP

An yiwa wasu manyan 'yan jama'iyar adawar Sudan 3 bulala 20 kowanne saboda tada zaune tsaye.

Wani kakakin Jama'iyar Sudanese Congress ta ce an same su da laifi ne, sannan aka yi masu bulala kafin lauyansu ya isa kotu.

Mutane ukun an kama su ne a cikin watan Afrilu bayan kiran da suka yi cewa, a kaurace wa zabe.

Shugaba Omar Al- Bashir, wanda ya kasance kan iko tun shekaru 26 da suka wuce ne ya lashe zaben.