'Yan IS sun kashe mutane a Syria

Image caption 'Yan IS na hallaka masu adawa da su

'Yan kungiyar IS a Syria ta saka wano hoton bidiyo a intanet yana nunin kisan masu fafutika biyu da suke samar da bayanai a kan halin da ake ciki a Raqqa, wanda yake babban birninsu.

Bidiyon ya nuna ana yi wa wasu mutane biyu tambayoyi daga nan aka daure su a wata itaciya, aka harbe.

Wani gungun masu fafutika na ta kokarin sanar da duniya a kan yadda kungiyar ta IS ke tafiyar da birnin.

Birnin ya kasance wani wurin kashe 'yan jarida da 'yan luwadi da kuma duk wani da suke gani a matsayin mai kiyayya ga kungiyar.