Bikin tunawa da hare-haren birnin London

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daya daga cikin bam din ya fashe na a cikin bus

An gudanar da hidimomi a London domin cika shekaru 10 da hare-haren da masu kishin Islama suka kai a kan hanyoyin sufuri na birnin wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 52.

Masu aikin ceto da iyalan wadanda suka mutu sun halarci taron addu'a a cocin St Paul's Cathedral.

Tun farko kuma Firaminista, David Cameron, ya ajiye furanni a dandalin tunawa da wadanda lamarin ya rutsa da su a Hyde Park a daidai lokacin da bam na farko ya tashi.

Bama-bamai hudu ne suka tarwatse a tashoshin jiragen kasa da wata motar bas.

A cikin wani sako don tunawa da zagayowar ranar, Mr Cameron ya ce, ta'addanci ba zai girgiza Birtaniya ba.