Al Shabab ta kashe mutane 14 a Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin alshabab

Kungiyar Al Shabab ta ce ta kai hari arewa maso gabashin Kenya inda akalla mutane 14 suka mutu.

Lamarin ya faru ne a yankin Mandera wanda ke kusa da iyakar Somaliya inda mafi yawancin 'yan kungiyar Al Shabab su ke zaune.

Mafi yawancin wadanda suka mutu ma'aikata ne a inda ake fasa duwatsu.

Mazauna yankin sun ce sun ji fashewar wasu abubuwa 2 a cikin dare, sai kuma suka ji harbe-harbe.

Kungiyar Al Shabab tana yawan kai hare-hare a Kenya kuma suna daukan mutane aiki.