An kai harin bam a Zaria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Har yanzu dai baubu cikakken bayani kan harin da aka kai a Zaria.

Rahotanni daga Zaria da ke jihar Kaduna a Najeriya na cewa an kai harin bam a ‪birnin ranar Talata.

Rahotannin sun ce ana zargin 'yan kunar bakin wake ne suka kai harin a lokacin da ake tantance ma'aikata a sakateriyar karamar hukumar Sabon Gari.

Har yanzu dai babu cikakken bayani a game da harin da kuma yawan mutanen da ya shafa.

A baya mutanen da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun sha kai hare-hare a birnin.