Bam ya kashe mutane 25 a Zaria — El-Rufai

Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Elrufai ya ce suna hada gwiwa da gwamnatin tarayya domin murkushe 'yan ta'adda

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce mutane 25 ne suka mutu sanadiyar harin da aka kai a Sabon Gari Zaria ranar Talata.

Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda kuma ya nuna rashin jin dadinsa da harin da 'yan ta'addan suka kai, lamarin da ya janyo jikkatar mutane 35.

Gwamna El-Rufai ya kara da cewa gwamnatin jihar Kaduna tana hada gwiwa da gwamnatin tarayya domin kawo karshen ta'addanci a jihar.

Daga bisani gwamna El-Rufai ya kai ziyara wajen da aka kai harin, inda ya jajantawa mutanen da lamarin ya shafa.

Lamarin ya faru ne bayan da a daren ranar Litinin a Kano, wata yarinya ta kai harin kunar bakin wake a daidai shataletalen 'Dangi' ta rasa ranta, a yayinda kuma mutum guda ya jikkata.

Harin ya auku ne wasu 'yan mintina bayan kammala sallar Taraweeh a wani masallaci da ke kusa da shataletalen a birnin Kano.