Za a soma biyan kudin kallon talabijin a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba John Mahama na Ghana

Daga watan Agustan bana, 'yan kasar Ghana za su dinga biyan kudin kallon talabijin kamar yadda ake yi a wasu kasashen duniya.

Tsarin na gwamnati ya nuna cewa mai talabijin daya a gidansa zai dinga biyan dala tara a duk shekara watau naira dubu biyu.

Sai kuma duk wanda ke da fiye da talabijin biyu a gidansa, zai dinga biyan naira 3,500 a duk shekara.

A shekara ta 2010 ne aka bullo da shirin amma aka dakatar saboda matsala wajen karbar kudin daga wurin jama'a.

Gwamnati ta ce kashi 72 cikin 100 na kudin kallon talabijin za a baiwa kafar yada labarai ta gwamnatin Ghana a yayinda za a baiwa kafafen yada labarai masu zaman kansu kashi 15 cikin 100.

'Yan Ghana sun nuna mamaki game wannan matakin, saboda a cewarsu shirye-shiryen kafafen yada labaran kasar ba sa kayatar da su.