EFCC ta kama Sule Lamido da 'ya 'yansa

Hakkin mallakar hoto google

Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin aziki zagon ƙasa ta kama Sule Lamido tsohon gwamnan jihar Jigawa tare da 'ya 'yansa biyu.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwajuren ta tabbatarwa BBC kamun tsohon gwamnan bisa zargin sama da faɗi da makuden kudade a lokacin mulkinsa.

Koda a karshen 2012 jami'an hukumar EFCC sun kama ɗaya daga cikin 'ya 'yan tsohon gwamnan yana shirin fita kasar waje da maƙuden kuɗaɗe.

A Najeriya gwamnoni su na da kariyar doka daga fuskantar tuhuma yayin da suke kan mulki.