Ebola: WHO ta gaza shawo kan cutar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana gwajin yanayin jiki a Laberiya

Wani rahoto a kan bullar cutar Ebola a yankin yammacin Afrika ya nuna cewar Hukumar lafiya ta duniya ba ta da karfin tinkarar lamuran lafiya na gaggawa a duniya.

Mutane fiye da dubu 11 ne suka mutu, kusan dukaninsu a Guinea da Saliyo da kuma Liberia sakamakon kamuwa da cutar Ebola.

Rahoton mai zaman kansa, wanda tsohuwar shugabar kungiyar bayar da agaji ta Oxfam ta hada, ya gano cewar martanin hukumar lafiyar ta duniya ya samu cikas ne sakamakon rashin kudi da kuma rashin samun isassun bayanai tare da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai rahoton ya ce, ba hukumar ce kadai za a dora wa laifi ba, inda ya kara haske a kan gazawar a cikin daukacin tsarin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya.