Chibok: Buhari zai gana da 'yan BBOG

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan kungiyar BBOG

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da 'yan kungiyar dake fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok, Bring Back Our Girls a ranar Laraba.

Tun bayan da aka rantsar da shi ne 'yan kungiyar suka rubuta wasikar nemam ganawa da shugaban, domin su tattauna hanyoyin ceto 'yan matan da aka sace a makarantar a jahar Borno fiye da shekara daya da ta wuce.

Dr Emman Shehu, daya daga cikin 'yan kungiyar ya bayyana niyyar gwamnatin Buhari ta ganawa da su a matsayin ci gaba.

Ya shaida wa BBC cewa sau uku suna rubuta wasika ga tsohuwar gamnatin Dr. Goodluck Jonathan amma basu samu nasarar ganawa da shi ba.

Baya ga 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace, kungiyar ta kuma sace wasu karin mutane da suka hada da yara.

Sojojin kasar da ke yaki da kungiyar a arewa maso gabshin kasar sun samu nasarar ceto wasu daga cikin mutanen da kungiyar Boko Haram din ta sace.