Boko Haram ta kashe mutane 20 a Chadi

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan Boko Haram sun addabi Nigeria, Chadi da Kamaru da kuma Nijar

Rahotanni daga Chadi na cewa mayakan Boko Haram sun hallaka mutane fiye da 20.

Hukumomi sun ce mayakan sun kaddamar da hare-haren ne a kauyuka biyu da ke kusa da tafkin Chadi.

A kauyen, Merom 'yan Boko Haram din sun yi wa maza 13 yankan rago a cikin dare.

Daga nan sai suka je kauye na biyu inda suka hallaka wasu makiyaya.

A cikin makwannin nan 'yan Boko Haram sun tsananta hare-hare a Nigeria.

Ta kai hare-hare a Chadi a cikin wannan watan musamman a Ndjamena babban birnin kasar.