An kama wanda ya kitsa hare-haren Jos da Zaria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin ta ce an kama mutumin ne lokacin wani samame da aka kai a Gombe.

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama mutumin da ya kitsa hare-haren da aka kai a biranen Jos da Zaria.

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an kama mutumin ne a garin Gombe lokacin wani samame da soji da jami'an hukumar tsaron farin kaya suka kai.

A ranar Lahadi ne dai aka kai hari a wurare biyu a birnin na Jos, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 50.

Kazalika, an kai hari a Sabon Gari, Zaria ranar Talata lokacin da ma'aikata ke jiran a tantance su, inda kimanin mutane 24 suka mutu.